Home Labarai Hajjin bana: Za a fara jigilar alhazan Nijeriya a ranar 15 ga watan Mayu — NAHCON

Hajjin bana: Za a fara jigilar alhazan Nijeriya a ranar 15 ga watan Mayu — NAHCON

0
Hajjin bana: Za a fara jigilar alhazan Nijeriya a ranar 15 ga watan Mayu — NAHCON

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON , ta ce a ranar 15 ga watan Mayu ne za a fara jigilar maniyyatan bana zuwa Saudiyya domin sauke farali.

Shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ne ya bayyana haka a jawabin buɗe taron masu ruwa da tsaki na farko da hukumar ta shirya a Abuja.

Arabi ya ce kimanin maniyyata 51,000 ne za su gudanar da aikin hajjin bana inda ya ce jiragen da suka samu sahhalewa ne za su yi jigilarsu zuwa ƙasa mai tsarki.

Shugaban hukumar ta Nahcon ya ce hukumar ta yanke cewa a bana, duka maniyyatan Najeriya za su yi aƙalla kwana huɗu a Madina kafin soma aikin hajji.

Ya ce an shirya taron ne domin inganta ayyukan hukumar na gudanar da aikin hajji.

BBC Hausa