Home Labarai Rundunar sojin Nijeriya ta fara shari’ar sojoji biyu akan bam din Tudun Biri

Rundunar sojin Nijeriya ta fara shari’ar sojoji biyu akan bam din Tudun Biri

0
Rundunar sojin Nijeriya ta fara shari’ar sojoji biyu akan bam din Tudun Biri

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj-Gen. Edward Buba, ya ce wasu jami’an sojin Najeriya biyu na fuskantar Shari’a a kotun soji dangane da harin bam din da ya faru Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Buba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Alhamis a Abuja kan ayyukan rundunar sojin kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya tuna cewa fararen hula 85 ne aka kashe a ranar 3 ga Disamba, 2023 bisa kuskure a harin da jiragen yaki mara matuki na sojoji suka kai a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Buba ya ce sojoji za su hukunta jami’an da aka samu da hannu a harin na ranar 3 ga watan Disamba, inda ya ce an gudanar da bincike tare da yanke shawarar tabbatar da cewa an gurfanar da jami’an da ake zargi a gaban kuliya, kuma an yi wa wadanda abin ya shafa adalci.

“Sojoji sun gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin kuma sun fara daukar matakin ladabtarwa a kan wadanda ke da laifi.

“Haka zalika, jami’an da abin da ake zargi za su fuskanci kotun soji bisa aikata laifi.

“Duk da haka bai kamata na yi magana game da lamarin ba batu ne da ke gaban kotu kuma bani da ikon yin magana.

“Sojoji za su yi taka-tsan-tsan nan gaba don tabbatar da cewa nan gaba harin ba zai sake shafar ƴan ba ruwa na ba,” in ji shi.