Home Labarai Gwamnatin taraiya za ta fara farautar ma’aikatan da suke da shaidar karatu ta bogi

Gwamnatin taraiya za ta fara farautar ma’aikatan da suke da shaidar karatu ta bogi

0
Gwamnatin taraiya za ta fara farautar ma’aikatan da suke da shaidar karatu ta bogi

Gwamnatin taraiya ta baiyana cewa za ta fara farautar ma’aikatan gwamnati da na ma’aikatu masu zaman kansu da ke aiki da takaddun bogi.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamma ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a lokacin da ya karbi rahoton kwamitin bincike na ma’aikatu kan takardar shaidar digiri na bogi daga shugaban kwamitin, Farfesa Jubrila Amin.

Mamman, wanda ya bayyana bacin ran sa kan abin da aka gano a yayin gudanar da bincike, ya ce ma’aikatar za ta hada hannu da hukumomin da su ka dace domin tsaftace fannin ilimi da kuma kawar da duk wata dabi’a ta bogi.

“Ba za mu bari wasu tsiraru gurɓatattu su bata harkar iliminmu ba. Mai yiyuwa ne wasu na aiki da takardun bogi a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, wadanda ya kamata a yi farautar su.

“Wannan rahoto ya samo asali ne daga cikakken bincike,” inji shi.

Ya ce: “Abin takaici ne a ce wanda ya kamata ya fito daga wata jami’ar Najeriya da sakamakon 2:1 ko 2:2 amma sai ya samo shaidar dogiri na karya kuma ya ci maki mafi girma, to ba za mu lamunta ba,” in ji shi.