Home Labarai Abba Gida-gida ga Ƴan shara: Ban kori kowa daga cikin ku ba kuma za ku ji ‘alert’ kwananan

Abba Gida-gida ga Ƴan shara: Ban kori kowa daga cikin ku ba kuma za ku ji ‘alert’ kwananan

0
Abba Gida-gida ga Ƴan shara: Ban kori kowa daga cikin ku ba kuma za ku ji ‘alert’ kwananan

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya musanta korar ma’aikatan shara kamar yadda ake ta yadawa a sassa daban-daban na jihar.

Gwamna Yusuf ya musanta hakan ne a jiya Lahadi, yayin wata ganawa da ya yi da wakilan ƴan sharar a gidan gwamnati.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin an samar da tsaftataccen muhalli da lafiya domin jin dadin mazauna jihar.

Gwamna Abba Gida-gida ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden alawus-alawus na ƴan shara da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.

“Bari in fada a baiyane. Ban kora ba kuma ba zan ba da umarnin korar wani daga cikin ku ba. Babu wani dalili da hakan za ta faru. A maimakon haka, mun dauki karin ma’aikata domin muhallinmu ya kasance da tsabta.

“A matsayina na ɗan kasa nagari wace riba zan samu ko wanne daɗin zan ji na kore ku daga abin da kuke yi don samun abincin yau da kullum”.

“Wannan taro ya zama wajibi la’akari da kukan da ake yi a kai a kai da kuma takaitaccen bayani mara dadi da na samu kan rashin biyan ku alawus-alawus.

“Ina so in tabbatar muku da cewa za ku karbi alawus din ku da wuri-wuri. Mun gano inda matsalar take tare da kawo karshen matsalar,” in ji shi.