
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a hukumance akan kudurin dokar tantance lafiyar ma’aurata kafin aure a jihar Kano, wadda ta tanadi duba lafiyar duk wadanda suke son aure.
Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar gwajin cututtukan kamar su ciwon hanta B da C, kanjamau, sikila da sauran cututtuka masu alaka da su, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa ya bayyana a wata sanarwa.
Ya ce dokar ta zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara da cututtuka.
Dokar, a cewarsa, ta yi daidai da kudurin gwamnatin jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga bangaren kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya.
Dawakin-Tofa ya ce dokar ta tilasta yin gwajin cutar kanjamau, Hepatitis, genotype, da sauran gwaje-gwajen da suka dace kafin aure.
“Dokar ta haramta duk wata wariya ko kyama ga mutanen da ke dauke da cutar kanjamau, sikila, ciwon hanta, da kuma wasu yanayi.
“A yayin rattaba hannun, Gwamna Abba
Kabir Yusuf ya jaddada cewa manufar aiwatar da dokar ita ce tabbatar da tsarkin aure a jihar Kano tare da tabbatar da haihuwar ‘ya’ya masu lafiya, ba tare da wata cuta ba.”
Ya kuma ce duk wanda aka samu da karya dokar, za a yanke masa tarar Naira dubu dari biyar ko shekara biyar a gidan gari ko kuma duka.