Home Labarai Idan mu ka yi rijista da CAC to akan kwastomomi za mu fanshe — Masu POS

Idan mu ka yi rijista da CAC to akan kwastomomi za mu fanshe — Masu POS

0
Idan mu ka yi rijista da CAC to akan kwastomomi za mu fanshe — Masu POS

Wasu masu sana’ar PoS, a babban birnin tarayya Abuja, sun koka kan sabuwar umurnin da hukumar kula da harkokin kamfanoni, CAC ta ba su na yin rajista da hukumar.

A ranar Litinin ne hukumar ta CAC ta bayar da wa’adin watanni biyu ga masu sana’ar PoS da su yi rajista wakilansu, diloli, da daidaikun mutane da hukumar kamar yadda doka ta tanada da kuma umarnin babban bankin Najeriya, CBN.

Masu POS din, wadanda suka zanta da NAN a Abuja a yau Laraba, sun ce rajistar, wanda sai sun biya kudi, zai shafi farashin cajin da kwastomomi ke biya.

Kofi Kolawole, mai sana’ar PoS, ya ce rajistar za ta rage ribar da ake samu a kasuwancin.

Kolawole ya ce rajistar za ta kuma hana mutane shiga harkar POS.