Home Labarai Majalisar Dattawa ta nemi a karasa aikin tagwayen titin Wudil-Gaya-Dutse

Majalisar Dattawa ta nemi a karasa aikin tagwayen titin Wudil-Gaya-Dutse

0
Majalisar Dattawa ta nemi a karasa aikin tagwayen titin Wudil-Gaya-Dutse

Majalisar Dattawa ta umurci kwamitinta manyan ayyuka da ya tuntuɓi Ministan Ayyuka domin kammala aikin tagwayen titin Wudil-Gaya-Dutse da ke kan titin Kano zuwa Maiduguri.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da Sanata Kawu Sumaila (NNPP- Kano) ya gabatar a zauren Majalisar a jiya Talata.

Da yake gabatar da kudirin, Kawu Sumaila ya ce titin babbar hanya ce mai matukar muhimmanci wajen jigilar mutane da kayayyakin noma a yankin Arewa.

Ya ce gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta bayar da kwangilar gina titin shekaru 17 da suka gabata.

Ya ce gwamnatocin da suka shude sun kasa kammala hanyar, inda ya yi kira da a hanzarta kammala aikin