
Wata karamar yarinya ta mutu yayin da mutane 15 su ka jikkata biyo bayan wata guguwar iska wacce ta kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira a Unguwar Southern Bypass da ke cikin birnin Gombe a jihar Gombe.
Jaridar City & Crime ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 5 na yamma a lokacin da aka yi ruwan sama na farko a Gombe, inda sama da gidaje 100 kuma suka lalace.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Ampate, Maitama, Nayi Nawa da Bagadaza dake wajen garin Gombe.
Wani mazaunin Bagadaza, Malam Abba Muhammad, ya ce rufin gidan sa mai daki biyu ya yaye, yayin da katangar gidan ta ruguje, lamarin da ya tilastawa iyalansa mai mutane biyar komawa gidan makwabta.
Shugaban gundumar Wuro Ampate, Malam Isa Adamu, ya ce lamarin ya sa iyalai da dama suka rasa matsuguni tare da yin illa ga rayuwar wasu da dama.
Ya ce, “Mun yi ta zagawa don gano adadin gine-gine da iyalan da abin ya shafa, amma ba mu iya samun takamammen adadin kadarorin da abin ya shafa ba saboda barnar ta yi yawa.
Wakilin jaridar ya ruwaito cewa, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta ziyarci yankunan domin tantance irin asarar da aka yi domin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.