
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yi alkawarin biyan kudin hadaya, Riyal 720 na kasar Saudiyya ga kowane mahajjaci daga jihar.
Radda ya kuma yi alkawarin bayar dajdon Barka Sallah da aka saba yi ga alhazan jihar a kasa mai tsarki.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da tawagar mutane 11 na jihar zuwa aikin Hajjin bana a karkashin jagorancin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Tukur Ahmed Jikamshi.
Gwamnan ya umurci tawagar alhazai da hukumar kula da jin dadin alhazai da su tabbatar da cewa ba a cire ko kobo daya daga cikin guzurin alhazai ba.
Ya bayyana farin cikinsa cewa duk da kalubalen da ake fuskanta a sakamakon karin kudin aikin Hajji da aka yi, alhazan jihar sun samu nasarar biyan kudin.
A cewarsa, tawagar jihar tana da hurumin kula da yadda za a gudanar da aikin Hajji daga farko zuwa karshe a bana.