
Dalilin da ya sa na bada sadakar likkafani, tukwane da motocin daukar gawa — Sanata Hanga
Sanata Rufa’i Sani Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya yi ƙarin haske a kan sadakar likkafani da tukwane da motocin daukar gawa da ga baiwa al’ummar yankin sa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne a ka riƙa caccakar Sanatan ta kafofin sadarwa bayan da hotuna suka baiyana na wasu tarin tukwane da likkafani, cewa daga gare shi ne ya bayar a matsayin aikin al’umma na mazaɓa.
Sai dai kuma a wani taron manema labarai da ya yi a jiya Lahadi a ofishin sa a Kano, Sanata Hanga ya nuna mamakin yadda aka rika caccakar sa akan aikin alherin da ya yi.
A cewar sa, ya bada waɗannan kayaiyaki ne bisa buƙatar da al’ummomin su ka tura masa sakamakon ƙarancin tukwane da likkafani da ake samu a lokuta da dama idan an yi rasuwa.
Ya ƙara da cewa “kuma wannan aiki ne na alkhairi da na gada tun daga kakanni na. Na tashi na ga ana wannan aikin a gidanmu. Shine ni ma na ke yi tun kan ma na zama Sanata.
“Lokacin da zan bada wannan taimakon ma, a hannun shugaban kwamitin maƙabartu na jiha, Dangoribar Kano, na danƙa kayan a gaban malamai da limamai da dagatai da masu unguwanni na bayar.
“Kuma hakan ba zai kashe min gwiwa ba domin nan gaba ma zan raba wasu tabarmi da dardumai ga masallatai a Kananan Hukumomi 15 da nake wakilta. Duk dai ina yi ne domin samun yardar Allah,” in ji shi.
Sanata Hanga ya kara da cewa ya yi aiyuka da dama da basa cikin kasafin kuɗi, a aljihun sa ya yi su, inda ya ce ya saka aiyuka da dama a cikin kasafin kudi na 2023.