
Mutum na farko da aka yi wa dashen ƙodar alade ya mutu wata biyu bayan yi masa aikin, kamar yadda asibitin da ya yi aikin ya bayyana.
Richard Slyman mai shekara 62 ya yi ta fama da ciwon ƙoda kafin a yi masa wannan tiyata a watan Maris.
Babban asibitin Massachusetts ne ya sanar da rasuwar tasa a ranar Lahadi, sai dai ba a tabbatar da ko mutuwar tasa na da alaƙa da tiyatar da aka masa.
Tiyatar da aka yi wa Mista Slayman ta shiga tarihi, saboda yadda aka yi ta kalau, ba tare da samun wata matsala ba, saɓani waɗanda aka sha yi a baya.
Dama dai bayanai sun ce Mista Slayman na fama da siga da kuma hawan jini.
A 2018, an taɓa sanya masa kodar mutum, amma sai ta fara ba shi matsala bayan shekara biyar.
Bayan an sa masa ta alade a ranar 16 ga watan Maris, likitansa ya tabbatar da cewa yanzu babu buƙatar a riƙa wanke masa ƙodar domin tana aiki yadda ya kamata.
BBC Hausa