Home Labarai Gwamnatin Taraiya za ta gina titin ‘bye-pass’ a Kano da wasu garuruwa a Arewacin Nijeriya

Gwamnatin Taraiya za ta gina titin ‘bye-pass’ a Kano da wasu garuruwa a Arewacin Nijeriya

0
Gwamnatin Taraiya za ta gina titin ‘bye-pass’ a Kano da wasu garuruwa a Arewacin Nijeriya

Majalisar zartaswa ta ƙasa ta amince da bada kwangilar ginin sabon titi da zai kewaye arewacin Kano, wanda a ka yi wa laƙabi da ‘Northern bye pass’.

A sanarwar da Abdulaziz Abdulaziz, kakakin Shugaban ƙasa ya fitar, akwai kuma ƙarin wasu ayyukan da majalisar ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta amince a aiwatar a jihohin Kebbi da Kwara da Kogi da kuma Abuja.

Sabon bye-pass ɗin na Kano wanda zai ratsa daga garin Dawanau ya ɓullo har zuwa Yankaba yana da tsahon kilometre 37 kuma babban kamfanin nan na CCECC ne zai gudanar da aikin.

Aikin zai lashe kuɗi har naira biliyan N230 kuma ana sa ran kammala shi cikin watanni 36.

A dai zaman nata na wannan mako, majalisar ta amince da farfaɗo da aikin babbar hanyar da ta tashi daga Sakkwato ta kai har Badagary a jihar Legas.

Tun a 1976 aka ƙirƙiri gina hanyar amma sai a ka yi watsi da aiwatar da ita tun bayan lokacin.

Haka nan kuma zaman majalisar ya amince da gina hanyar da ta tashi daga Ngaski zuwa Wara a jihar Kebbi.

Sai kuma aikin tsohuwar hanyar Abaji zuwa Koton Karfe da ta haɗa jihar Kogi da Abuja, da hanyar Kaima zuwa Teisse a jihar Kwara.