Home Labarai Mahaifi ya kai ɗansa kotu domin ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Kano

Mahaifi ya kai ɗansa kotu domin ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Kano

0
Mahaifi ya kai ɗansa kotu domin ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Kano

Wani fusataccen mahaifi ya yi ƙarar dan cikinsa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano.

Mahaifin ya koka da cewa ɗan nasa ya addabar shi da sace- sace da kuma shaye-shaye.

Mahaifin, w}}anda aka boye sunansa ya nemi kotun ta ɗaure ɗan nasa har illah ma sha Allah.

Mai gabatar da kara, Abdul Wada, ya karanta wa wanda ake ƙarar tuhume-tuhumen da ake masa, inda nan take ya amsa laifinsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Umar l Lawan Abubakar, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2024 don yanke hukunci.