
A yau Alhamis ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa birnin N’Djamena na kasar Chadi domin halartar bikin rantsar da Mahamat Deby a matsayin shugaban ƙasar Chadi.
Za a rantsar da Deby ne bayan ya lashe zaɓen shugaban kasa da aka yi a farkon watan nan, wanda babbar kotun kasar ta tabbatar da shi.
A sanarwar da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaban ƙasa Tinubu zai samu tsakiyar manyan jami’an gwamnati.
Sanarwar ta ce Tinubu zai dawo gida Nijeriya bayan an kammala bikin.