Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Majalisar Dokoki ta rushe masarautun Kano biyar da Ganduje ya ƙirƙira

DA ƊUMI-ƊUMI: Majalisar Dokoki ta rushe masarautun Kano biyar da Ganduje ya ƙirƙira

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Majalisar Dokoki ta rushe masarautun Kano biyar da Ganduje ya ƙirƙira

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartas da dokar majalisar masarautun Kano ta shekarar 2024 a yau Alhamis.

Wannan ya biyo bayan tattaunawar da aka yi a majalisar gidan yayin zaman ta na yau Alhamis.

Dokar da aka zartar bayan kammala karatu na 3 ta rushe ɗaukacin masarautu 5 a jihar.

Sabon kudirin dokar zai mayar da masarautar jihar zuwa tsohon tsarinta na sarki daya kamar yadda yake cewa an rushe ofisoshin da aka kafa a karkashin dokar da aka kafa a baya.

Kudirin ya kuma tanadi cewa duk hakimai da aka daga likkafar su ko aka nada a karkashin dokar da aka soke za su koma kan matsayin su na da.

Shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazabar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya miƙa ƙudirin dokar mai suna ‘Kano State Emirates Council (Amendment number 2) Law, 2024’.

A tuna cewa dokar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya wa hannu a ranar 5 ga watan Disamba, 2019, ta amince da dokar da ta kafa sabbin masarautu guda biyar a jihar sannan ta kori Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ko.

Majalisar ta kuma amince da kudirin kafa sabuwar masarauta mai daraja ta biyu a jihar.