Home Labarai Mataimakin gwamnan Kano ya nemi afuwar Ribadu kan zargin hannu a rikicin masarauta

Mataimakin gwamnan Kano ya nemi afuwar Ribadu kan zargin hannu a rikicin masarauta

0
Mataimakin gwamnan Kano ya nemi afuwar Ribadu kan zargin hannu a rikicin masarauta

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam ya nemi afuwar mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Nuhu Ribadu bisa zargin sa da gwamnatin ta yi na kitsa rikicin masarautar Kano.

Masarautar dai ta fada cikin rikici tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a dokar da majalisar dokokin jihar ta yi na rusa masarautu biyar da kuma dawo da Sarki Muhammadu Sanusi ll.

Sarkin Dawaki Babba ne dai ya kai ƙara cewa kotu ta dakatar da rushe masarautu da dawo da Sarki Sanusi.

Ana tsaka da haka sai aka ga tsigaggen Sarki Aminu Bayero, wanda ba ya jihar lokacin yin dokar, ya shigo har ya sauka a gidan Sarki na Nassarawa.

Tun daga nan ake ta dambaruwa akan wanene Sarki tsakanin Bayero da Sanusi ll.

Da ya ke zangawa da manema labarai a gidan Sarki, mataimakin gwamnan ya zargi Ribadu da cewa shine ya sa aka kawo Bayero da nufin ya koma kan kujerar sa.

Sai dai kuma Ribadu ya ƙaryata zargin inda ya kuma nemi Abdulsalam da ya fito ya bashi hakuri ko kuma ya kai shi kotu.

Sai dai kuma a zantawar sa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar a jiya Lahadi da daddare, Abdulsalam ya baiwa Ribadu hakuri tare da cewa rahoton da aka basu ne ya nuna cewa NSA din ne ke da hannu a rikicin.

“Sai dai kuma bayan ya nisanta zargin, mun yi tunanin cewa a yadda muka san Ribadu, inda da hannun sa to na zai boye ba.

“Saboda muna bashi hakuri a bisa abinda muka fada kuma za mu ci gaba da bashi hadin kai na bayanai domin samun nasarar aikin sa na NSA,”

Mataimakin gwamnan ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sa baki domin kawo karshen rikicin a jihar domin samun zaman lafiya.