
Wata Babbar Kotun jiha, karkashin Mai Shari’a Amina Aliyu ta hana tuɓaɓɓen Sarki Aminu Ado Bayero daga nuna kan sa a matsayin Sarkin Kano .
Tun a ranar Juma’a da daddare ne dai Aminu ya shigo Kano kuma ya wuce gidan Sarki na unguwar Nassarawa bayan da wani mai rike da mukamin a tsakiyar fadar sa ya shigar da kara a kan rushe masarautu biyar da gwamnatin jihar Kano ta yi.
A yayin da ta bada umarnin a yau Litinin, Mai Shari’a Amina ta ce dukkan sarakuna biyar din da aka rushe kar su sake yin wani abu a matsayin sarakuna.
Ta kuma baiwa Kwamishinan Ƴansanda na jihar umarnin fitar da Aminu Ado Bayero daga gidan da yanke ciki a halin yanzu.