
Gwamnatin tarayya ta kara naira dubu 3 a kan tayin da ta fara yi na biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 57 wanda hakan ya zama naira dubu 60 da ta gabatar a ranar Talata a wajen wani taro na kwamitin koli kan mafi karancin albashin ma’aikata a Abuja.
Kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar ‘Trade Union Congress’ da ‘Nigerian Labour Congress’ suma sun rage Naira dubu 3 daga tayin karshe na Naira dubu 497.
A cewar wata majiya da ta yi karin haske a taron na ranar Talata, adadin da gwamnati ta gabatar bai yiwa shugabannin kwadago dadi ba.
Wani mamba a kungiyar da ya zanta da wakilin PUNCH kafin a fara taron ya bayyana cewa NLC ta yi rafin ne yayin da gwamnati ta yi ƙari.
“Wannan lamari ne kawai idan sun hau sama, za mu rage. Suna bukatar su yi wani abu mai ma’ana don muma mu rage namu adadin,”