Home Labarai Tun kafin ya fara aiki, an kori kocin tawogar ƙwallon ƙafar Cameroon bayan cacar-baki da Eto’o

Tun kafin ya fara aiki, an kori kocin tawogar ƙwallon ƙafar Cameroon bayan cacar-baki da Eto’o

0
Tun kafin ya fara aiki, an kori kocin tawogar ƙwallon ƙafar Cameroon bayan cacar-baki da Eto’o

Cameroon ta maye gurbin koci, Marc Brys ba tare da ya ja ragamar wasa ko ɗaya ba – bayan cacar baki da shugaban hukumar ƙwallon kafar kasar, Samuel Eto’o.

An sanar da naɗa, Martin Ndtoungou a matakin kociyan riƙon ƙwaryar tawagar ta Indomitable Lions a wani taron gaggawa na kwamitin hukumar ta Fecafoot.

A wani jawabi da hukumar ta fitar ta ce ”Ta sallami, Brys saboda kalaman rashin girmamawa da wasu halayya marasa ƙyau daga kocin da mataimakansa.”

Cikin watan Afirilu ma’aikatar wasanni ta Kamaru ta naɗa Brys sabon kociyan Indomitable Lions, amma hukumar ƙwallon kafar kasar ta nuna ɓacin ranta kan matakin.

Eto’o tsohon ɗan wasan Barcelona da Inter Milan da kuma Chelsea ya tanadi sunayen fitattun kociyan da ya kamata a tuntuba, amma tun kan ya gabatar da su domin yin zawarcin aiki, sai ya ji an ɗauki Brys, mai shekara 62.

Eto’o da Brys sun hadu a hukumar ƙwallon Kamaru a Yaounde ranar Talata, sai dai wani bidiyo a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da suke cacar baki a tsakaninsu daga baya kociyan ya yi tafiyarsa.

An kuma ga Eto’o, wanda ke jan ragamar shugabancin Fecafoot tun cikin Disambar 2021 na tattaunawa da jami’an ma’aikatar wasannin da yadda suka samu rashin jituwa.

BBC Hausa