Home Labarai Tinubu ya tabbatar da dawo da tsohon taken Nijeriya ” Nigeria We Hail Thee”

Tinubu ya tabbatar da dawo da tsohon taken Nijeriya ” Nigeria We Hail Thee”

0
Tinubu ya tabbatar da dawo da tsohon taken Nijeriya ” Nigeria We Hail Thee”

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi rattaba hannu a kudurin dokar taken Nijeriya ta 2024, wanda ya ke da taken “Nigeria We Hail thee”, a matsayin sabon taken Nijeriya da ya maye gurbin “Arise O Compatriots”.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan a yau Laraba a yayin zaman haɗaka na majalisar kallon ƙasar domin murnar cika shekaru 25 a kan mulkin dimokuraɗiyya.

Majalisar ta rera taken kafin zuwan shugaban ƙasa da mataimakin sa Kassim Shettima da sauran manyan gwamnati.

Tuni dai ƴan su ka fara caccakar Tinubu a kafafen sadarwa, inda suke nuni da a samar da abinci a wannan muhimmiyar rana ba taken Nijeriya ba.