
Wani ɗansanda a jihar Bayelsa ya harbe wani direba har lahira mai suna Benalayefa Bako Asiayei, bisa zargin ya hana shi cin hancin Naira 200.
Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a kan titin Azikoro da ke Yenagoa a jihar ta Bayelsa.
Daily Trust ta ce har yanzu ba ta samu sunan ɗansandan ba, wanda ya ke cikin rundunar ƴansanda da ke sintirin ‘Operation Doo Akpo’.
An ce Asiayei, mai shekaru 40, wanda ya ke gyaran wutar lantarki, yana yin haya da motar sa ne a ranar da lamarin ya faru.
An ce an harbe shi ne a motar sa kirar Sienna lokacin yana kokarin daukar fasinja.
Shaidun gani da ido sun ce ƴansanda ne, a yayin sintiri da suke yi na binciken ababen hawa sai suka bukaci ya basu N200, inda a yayin da yake kokarin fada musu cewa fasinja daya kawai ya dauka, sai daya daga cikin yansandan ya harbe shi.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar na jihar, ASP Musa Muhammed, ya ce zai fitar da sanarwa a kan lamarin.