
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya koka kan yadda Arewacin Nijeriya ke fama da talauci da lalacewar ababen more rayuwa, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci hakan ba.
Ya kuma yi kira ga shugabanni a kasar nan da su gargaɗi gwamnonin jiha da su ci gaba da zama a jahohinsu don aiwatar da kyakkyawan shugabanci ga al’umma a matakin jiha.
Tinubu, wanda ya kuma koka da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar, ya yi kira da a hada karfi da karfe domin shawo kan matsalar.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin Kungiyar Tuntuba ta Arewa, ACF, a fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja, a jiya Alhamis.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su ba da fifiko ga bukatun al’ummomin kananan hukumomi ta hanyar tabbatar da bin diddigin al’amuran da suka shafi gudanar da kananan hukumomi.
“Zan yi kira gare ku da ku tsawatar wa gwamnonin Ina yin iya kokarina don inganta samun kudaden shiga na kasa. Dole ne su kasance masu tausayi, kuma su yi la’akari da bukatun jama’ar yankin cikin gaggawa,” in ji Tinubu