Home Labarai DSS sun kama ɗaya daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

DSS sun kama ɗaya daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

0
DSS sun kama ɗaya daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) a Kano sun kama daya daga cikin wadanda su ka shirya yin garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Daily Trust ta tattaro cewa jami’an sun kuma kashe mutum daya da ake zargi a wani samame da suka yi a boye.

A cewar wata majiya mai karfi a rundunar, an kuma ƙwato Naira miliyan 26.5 a yayin sumamen.

Majiyar ta ce, rundunar DSS a jihar Kano, bisa ingantattun bayanan sirri ta kama wasu gungun ‘yan bindiga biyar a dajin Makarfi inda suke raba kudin fansar.

“Wani Hamisu Tukur, a halin yanzu yana tsare da raunukan harbin bindiga a jikin sa, yayin da aka kashe Bature,” in ji majiyar.