
Matasan Arewa, ƙarƙashin ƙungiyar Gamaiyar Kungiyoyin Matasan Arewa sun yi kiran gaggawa ga Gwamna Umaru Mohammed Bago na Jihar Neja da ya bincika dambarwar da ke faruwa tsakanin kungiyar INCRESE da wani ɗan gwagwarmaya, Sai Baba.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Rundunar ƴansanda a jihar Neja ta tsare wani mai fafutuka kuma mai sharhi kan al’amuran zamantakewar al’umma a garin Minna, Muhammad Yahaya Usman, bisa zarginsa da wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya bukaci a gudanar da bincike kan ayyukan wata kungiya mai zaman kanta.
Ƙungiyar, mai suna, Cibiyar Kare Lafiya da Hakkin Jima’i ta Ƙasa da Ƙasa, INCRESE, na rajin kare hakkin jima’i ne ga mata.
Usman, wanda aka fi sani da Sai Baba, ya yi zargin cewa kungiyar na yada ayyukan ƙungiyar auren-jinsi ta duniya, LGBT ne kuma ya yi kira ga gwamnatin jihar Neja da ta binciki ayyukansu da kuma hanyoyin da su ke samun kudaden.
A wani sako da ya wallafa a Facebook bayan an sake shi, Usman ya ce a maimakon mayar da martani ga batutuwan da ya wallafa, sai kungiyar ta shigar da kara a kan zargin bata masa suna a sashin binciken manyan laifuka na jihar, SCID.
Da ya ke zanta wa da manema labarai a Abuja, Shugaban Kungiyar Matasan, Comrade Hamza Saulawa yace “idan babu rami meya kawo rami? shin me yasa kungiyar ta tunzura don kawai Sai Baba ya tuhumesu kan aikace-aikacen ta.?”
Ya ce daukar matakin zai taimaka wurin hana al’umma faɗa wa cikin ribatar shaidanu.