Home Labarai Dan Majalisar Wakilai ya gwangwanje ƴarsa da kyautar mota don murnar kammala karatun sakandire

Dan Majalisar Wakilai ya gwangwanje ƴarsa da kyautar mota don murnar kammala karatun sakandire

0
Dan Majalisar Wakilai ya gwangwanje ƴarsa da kyautar mota don murnar kammala karatun sakandire

Mamba mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Gagdi, ya baiwa ƴarsa kyautar dalleliyar mota kirar Lexus RX, crossover SUV, domin murnar kammala karatun sakandire tare da samun maki mai kyau a jarrabawarta ta shiga jami’a, UTME.

Ƴar ta sa mai suna Aisha Gadgi ta kammala karatunta a makarantar Lead British International School Abuja a jiya Asabar.

Wani shahararre a Facebook, Saminu Maigoro, ya wallafa hotunan matashiyar tare da mahaifinta, suna baje kolin motar ta alfarma.

“Ina taya Aisha Yusuf Gagdi murnar kammala karatunki a makarantar Lead British International School Abuja. Allah Ya sa hakan ya zama mafarin ci gaban ki a rayuwa.

“Don murnar kammala karatun ta da kuma rawar da ta taka a JAMB, mahaifinta ya ba ta mamaki da kyautar mota,” in ji Mista Maigoro.

Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta lura cewa kyautar ta janyo cecekue a shafukan sadarwa, inda wasu su ke goyon bayan hakan, wasu kuma su ke alla-wadai duba da matsin rayuwa da ƴan Nijeriya ke ciki.