Home Labarai Tinubu ga masu zanga-zanga: Ina rokon ku da ku tsagaita ku zo mu tattauna

Tinubu ga masu zanga-zanga: Ina rokon ku da ku tsagaita ku zo mu tattauna

0
Tinubu ga masu zanga-zanga: Ina rokon ku da ku tsagaita ku zo mu tattauna

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi wadanda su ka shirya zanga-zangar matsin rayuwa da ke gudana a faɗin Nijeriya da su tsagaita haka su kuma zo a tattauna da su don shawo kan lamarin.

Da ya ke jawabi ga ƴan ƙasa a safiyar yau Lahadi, Tinubu ya ce ya kaɗu tare da alhinin rikici da ya faru a wasu jihohin a yayin zanga-zanga.

“Na kadu tare da alhinin abubuwan da su ka faru a Kano, Jigawa, Kaduna da sauran jihohi. Kone-kone da fashe-fashe da sace-sacen kayan gwamnati da na al’umma, saɓanin alkawarin da masu shirya zanga-zangar su ka yi. Wannan ya janyo mana ci baya saboda da kuɗin al’umma za a yi amfani wajen gyara barnar,”

Tinubu ya kuma jajanta tare da ta’aziyya ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukansu a zanga-zangar, inda ya jaddada cewa “dole a tsayar da zubar da jinin nan.”

“A matsayi na na shugaban kasa, dole na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma bisa ikon da kundin tsarin mulkin ƙasa ya bani. Gwamnati na ba za ta zuba ido wasu tsirari masu mummunar manufa su raba mana ƙasa ba.

“A halin yanzu, ina mai kira ga wadanda su ka shirya zanga-zangar nan da su tsagaita haka. Su zo mu zauna da su kamar yadda a ko da yaushe na ke bada kofar tattaunawa domin a samu maslaha.

“Ni buri na shine na samar da kasa wacce ko wanne dan kasa zai samu kwanciyar hankali da tsaro da jin dadi yadda zai dakata ya wala,” in ji Tinubu.