
Wasu majiyoyi daga hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa ƴan ƙungiyar Shi’ah ne ke ɗaga tutar kasar Russia a yayin zanga-zangar da ake gudanarwa a fadin Nijeriya.
Jaridar THE WHISTLER ta rawaito cewa wasu majiyoyi daga hukumomin tsaro sun tabbatar mata da cewa binciken su ya tabbatar musu da cewa ƴan Shi’ah ne ke da hannu wajen amfani da tutar ta Russia tun ranar da aka fara zanga-zangar a ranar 1 ga watan Agusta.
Jaridar ta kara da cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar mata da cewa ƴan ƙungiyar ta Shi’ah ne ke daga tutar su na kuma kira ga shugaban Russia, Vladimir Putin da ya kawo wa Nijeriya ɗauki, su ka riƙa kira da a yi juyin mulki a yayin zanga-zangar a Kano, Abuja, Jos da kuma Kaduna.
A cewar jaridar, ko a ranar Asabar, duk da dokar hana fita da gwamnatin Kano ta saka, sai da su ka fito, inda su ka saje da sauran masu zanga-zanga, su ka rika daga kwalaye da rubuce-rubuce da ke kira da Russia ta karɓe iko da mulkin Nijeriya.
Irin haka ne ya faru a Abuja, Jos, Kaduna da sauran jihohin Arewa a yayin zanga-zangar, in ji jaridar.
Da ya ke tsokaci kan lamarin, Shugaban Sojin Nijeriya, CDS, Christopher Musa ya yi gargaɗi da cewa ɗaga tutar wata ƙasa a yayin zanga-zangar laifin cin amanar ƙasa ne.
CDS ya baiyana haka ne jim kaɗan bayan ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a yau Litinin.
Ya kuma gargaɗi masu kiran a yi juyin mulki, inda ya ce sojojin Nijeriya sun gamsu da dimokradiyya kuma shi za a ci gaba da yi a ƙasar.