Home Labarai Shirin bashin ɗalibai: NELFUND ta raba lamunin wata-wata ga ɗalibai 20,371 a jami’o’i 6

Shirin bashin ɗalibai: NELFUND ta raba lamunin wata-wata ga ɗalibai 20,371 a jami’o’i 6

0
Shirin bashin ɗalibai: NELFUND ta raba lamunin wata-wata ga ɗalibai 20,371 a jami’o’i 6

Asusun Bada lamuni na Ilimi na Ƙasa, NELFUND ya sanar da bayar da tallafin Naira 20,000 na wata-wata, na watan Yuliga dalibai 20,371 a jami’o’i shida na kasar.

An bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan Kudi da Asusu na NELFUND, Ibom Uche, ya fitar a yau Litinin.

Uche ya lissafa daliban jami’o’in da suka amfana da su ka hada da Jami’ar Bayero Kano; Jami’ar Tarayya, Dutsin-Ma; Jami’ar Ilorin; Jami’ar Benin; Jami’ar Ibadan; da Jami’ar Maiduguri.

Ya ci gaba da cewa: “Wannan shiri na kara jaddada alkawarin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na tallafa wadaliban Najeriya ta hanyar tabbatar da ba su shiga fatara ba a duk lokacin da su ke neman ilimi.

“NELFUND na aiki tuƙuru don fara aiwatar da biyan kuɗin ga ɗalibai daga ƙarin manyan makarantu kusan 55 nan gaba kaɗan.

“Ana sa ran za a kammala hakan nan da makwanni biyu masu zuwa domin Asusun ya himmatu wajen ganin duk daliban da suka cancanta sun samu alawus dinsu cikin gaggawa,” in ji shi.