
Wata sabuwar cutar diphtheria da akafi sani da mashako ta lakume rayukan mutane sama da 40 yawancinsu kananan yara ne a jihar Kano,da dama na kwance a asibiti domin kulawar likita.
Daily Trust ta rawaito cewa a lokacin da ta ziyarci asibitin masu fama da cututtuka masu yaɗuwa (IDH) a jiya Laraba da misalin karfe 2:00 na rana, dukkan sassa uku na asibitin sun cika makil da majinyata, inda wasu da dama kuma suna kan layi domin ganin likita.
Wani jami’in asibitin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ba da rahoton adadin masu mutuwa a kullum sakamakon barkewar cutar, inda ya ce ya kai sama da 40.
“A makonni biyu da suka gabata, ana samun mace-mace a kullum daga masu fama da wannan cutar,” kamar yadda jami’in ya shaida wa Daily Trust.
Ya ce a kowace rana, likitoci suna duba adadin marasa lafiya. Idan ka ziyarta da safe ko da yamma, za ka tarar da dimbin wadanda ke fama da cutar suna jiran magani. Asibitin na ci gaba da karbar narasa lafiya tun bayan barkewar cutar.
Jami’in ya bayyana cewa asibitin ya cika makil saboda yawancin asibitocin kananan hukumomi ba su da kayan aikin da za su iya kula da irin wadannan matsalolin. Ya kara da cewa mafi yawan marasa lafiya ana tura su nan ne saboda wurin da muke aiki shi ne mafi kayan aiki don magance cututtuka masu yaduwa kamar haka.
Wata uwa mai suna Samira Danzaki wadda ‘yarta ke jinya a asibiti ta shaida wa Daily Trust cewa ta shafe kwanaki biyu a asibitin. Ta kawo ‘yarta a ranar Lahadi bayan ta kamu da zazzabi mai tsanani kuma wuyanta ya kumbura,an kai su wannan asibiti, kuma yanzu haka tana samun lafiya.