Home Labarai Saudiyya za ta hana masu matsananciyar rashin lafiya zuwa aikin Hajjin 2025

Saudiyya za ta hana masu matsananciyar rashin lafiya zuwa aikin Hajjin 2025

0
Saudiyya za ta hana masu matsananciyar rashin lafiya zuwa aikin Hajjin 2025

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar da sabbin sharudda na kiwon lafiya don tabbatar da tsaro da walwalar mahajjata, musamman ga maniyyata masu fama da wasu cututtuka.

Mutanen da ke fama da matsananciyar rashin lafiya ba za a ba su izinin gudanar da aikin Hajjin 2025 ba, kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Addini ta ƙasar, Muhammad Umar Butt ya bayyana.

Ya ce wannan matakin na da nasaba ne da yanayin tsananin zafi da rana da ake tsammanin za a yi a lokacin aikin Hajji, da kuma tabbatar da tsaro da kare lafiyar dukkan mahajjata.

Kakakin ya kara da cewa ba za a bar masu fama da matsanancin ciwon koda, zuciya, huhu, ciwon hanta da kuma ciwon daji ba su shiga aikin Hajji.

Bugu da kari, ya ce za a hana mutanen da suka kamu da cutar mantuwa , ko cututtuka masu yaduwa kamar su tarin fuka, tari, da sauran cututtuka makamantan haka yin aikin hajjin na badi.