
Masu kutse sun kwace shafin hukumar Hisbah ta jihar na Facebook inda su ke wallafa hotuna da bidiyoyi na batsa.
Kutsen wanda aka yi shi a ranar Laraba, ya jawo damuwa ga al’umma da jami’an hukumar Hisbah.
Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tabbatar da cewa an yi kutse a shafin, inda ya ce “Hukumar Hisbah ta jihar Kano tana sane da cewa an yi kutse a shafinta na Facebook, kuma ana dora abubuwan da basu dace ba.
“A madadin hukumar, ina kira ga jama’a da su taimaka a shawo kan wannan matsala”.
Ya tabbatarwa da jama’a cewa sashin fasahar zamani na hukumar na aiki wajen dawo da shafin kuma suna tattaunawa da kamfanin Meta wanda shi ne mallakin Facebook.
Daurawa ya bukaci al’umma da su aika rahotan korafin shafin da aka yiwa kutse domin dakatar da sanya abubuwan da basu dace ba.
Sani Zailani, shugaban sashin ICT na Hisbah ya ce a kwanakin baya shafin ya fuskanci irin matsalar kuma ya tuntubi kamfanin Meta kan kutsen na baya bayan nan inda suka yi alkawarin gyarawa cikin awanni 48.
Sannan ya yaba da goyan baya da damuwa da al’umma suka nuna kan lamarin inda yayi bayani kan kokarin da ake yi wajen dawo da shafin.