Home Labarai Legas: Ƴansanda sun kama samari biyu bisa yiwa wasu mata masu zaman kansu fashi

Legas: Ƴansanda sun kama samari biyu bisa yiwa wasu mata masu zaman kansu fashi

0
Legas: Ƴansanda sun kama samari biyu bisa yiwa wasu mata masu zaman kansu fashi

Rundunar ƴansanda a jihar Legas ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yi wa wasu mata masu zaman kansu su uku fashi.

Kakakin rundunar ƴansandan, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da kamen ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a yau Asabar.

Mista Hundeyin, mai muƙamin Sufeton ƴansanda, ya ce matan ne su ka kai a ranar Laraba da misalin karfe 2:20 na dare.

Ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun bayyana cewa sun hango wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fashi a wani wuri da ba a bayyana ba, wadanda ake zargin sun yi musu fashin kayan su a ranar 23 ga watan Agusta da misalin karfe 4:30 na asuba.

“Sun ce ƴan fashin biyu ne suka dauke su da niyyar za su je su kwana da su a unguwar Adeniran Ogunsanya, Bode Thomas, Surulere.

“Bayan sun kai su inda waɗanda ake zargin su ka ce sun kama, nan take sai su ka tsaya a motar da su ka dauko su, inda su ka ce su basu duk abinda ke tare da su da suka haɗa da wayar hannu korar Iphone guda biyu da kudinsu ya kai Naira miliyan 1.05, da kuma waya korar REDMI Note 12 wacce kudin ta ya kai N140,000, Iphone SR da ta kai N240,000.

Kakakin ‘yan sandan ya ce a yayin gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Ya bayyana cewa an kwato motar wadanda ake zargin, kirar Toyota Camry mai lamba APP335 JA, da sauran kayayyaki.