Home Labarai Tuntuni Tinubu ya gano cewa Buhari ba ya yin shi a zaɓen 2023 — Sule Lamido

Tuntuni Tinubu ya gano cewa Buhari ba ya yin shi a zaɓen 2023 — Sule Lamido

0
Tuntuni Tinubu ya gano cewa Buhari ba ya yin shi a zaɓen 2023 — Sule Lamido

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya bayyana cewa tun da fari , shugaban kasa Bola Tinubu ya gane cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ya yin shi.

Lamido, jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana haka a wata hira da jaridar Nigerian Tribune.

Ya ce: “Kafin babban taron jam’iyya na ƙasa, Tinubu, a garin Abeokuta na jihar Ogun, ya bugi kirji da cewa lokaci ya yi da zai mulki Najeriya, shi kuma Buhari yana kallo. Bai taba son Tinubu ba. Akwai wanda yake so.

“Bai aminta da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ba ma; Ahmed Lawan ya ke so, amma lissafinsa bai yi ba. Kun jagoranci Arewa shekara takwas, kuna son wani dan Arewa ya kara shekaru takwas?! A’a, watakila daga baya amma akwai wasu abubuwan da ba za ku iya canza ssu ba, ba a Najeriya ta yau ba.

“Shugaban Najeriya, bayan ya shafe shekaru takwas yana mulki, bai da karfin gwiwa wajen tsayawa kan zabin da ya yi. Yana can wajen taron kuma Tinubu wanda bai taba so ba, bai taba yarda ya fito ba. Tinubu ya san cewa nasararsa ba daga Buhari ba ce, don haka Buhari bai tsinana masa komai ba,” in ji Lamido.