
Gawurtaccen dan daban nan da ya addabi al’umma a jihar Kano, Abba Barakita ya mutu.
Rahotanni sun baiyana cewa Burakita ya riga mu gidan gaskiya ne bayan da al’umma su ka cafke shi a yayin da ya jagoranci ƴan daba su na yi wa jama’a kwacen waya a kan titin gidan gwamnati a makon da ya gabata.
Sai dai an ce Burakita ya mutu ne a asibitin Murtala da ke Kano inda yake karbar magani bayan raunin da ya samu lokacin da fusatattun mutane su ka yi masa duka.
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da mutuwar ta Burakita ga manema labarai.
Idan za a iya tunawa dai, a bara, Burakita wanda ya addabi al’ummar yankin Dorayi l, ya miƙa kansa ga rundunar ƴansanda baya ta aiyana neman sa da wasu su tara ruwa a jallo.