
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wata ganawa da shugaban ƙasar China Xi Jinping a yau Talata.
Ganawar ta wakana ne a Beijing, babban birnin ƙasar ta China.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun shugaba Tinubu, Ajuri Naglale ya ce shugabannin biyu sun amince da yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu zuwa matakin amintaka.
A cikin bayaninsa, shugaba Tinubu ya ce “Wannan ziyara ce mai matuƙar muhimmanci ga Najeriya da kuma Afirka baki ɗaya, kasancewar na zo nan ne a matsayi na na shugaban ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen Afirka (Ecowas).”
“Dangantakar da ke tsakanin Najeriya da China ta daɗe, kimanin rabin ƙarni, saboda haka akwai buƙatar a ƙara ƙarfafa wannan dangantaka domin bunƙasa harkar kasuwanci da ci gaban tattalin arziƙi,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa akwai damarmaki sosai a Najeriya kasancewar ta ƙasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, wadda kuma ke da ɗinbin matasa da za su taimaka wajen ciyar da tattalin arziƙi gaba.
Tinubu na ziyara ne a China a domin halartar taron bunƙasa hulɗa tsakanin ƙasashen Afirka da China.