
Olatunbosun Oyintiloye, wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, ya roki shugaban kasa Tinubu ya yi saurin daukar mataki kan karuwar yunwa da matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan.
Mista Oyintiloye, wanda tsohon dan majalisa ne yayi rokon yayin ganawa da manema labarai a birnin Osogbo a ranar Lahadi.
Ya ce wahalar rayuwa da yunwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta a yanzu na bukatar a dau matakan gaggawa.
Ya ce duk da cewa babu makawa, shugaban kasa Tinubu na aiki tukuru don kawo karshen wahalar da ake fuskanta, amma akwai bukatar kari.
Mista Oyintiloye, wanda mamba ne a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya ce matsin tattalin arziki da ake fuskanta shi ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da na mai da wutar lantarki.
Daga karshe ya roki ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bada goyan baya ga gwamnatin shugaban kasa Tinubu.