
Wasu jami’an Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS) da na Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) da aka tura kan iyakokin Najeriya sun koka da rashin biyansu alawus-alawus din su na tsawon shekaru biyu da rabi, lamarin da ya bar su cikin wani mawuyaci.
Ma’aikatan sun yi ikirarin cewa sun shafe sama da shekaru biyar su na aikin tsaro a kan iyakokin, tun daga gwamnatin da ta gabata; al’amarin da suka ce ba a saba gani ba ne kuma ga kashe musu karsashin aikin.
Daily Trust ta rawaito cewa daya daga cikin jami’an tsaron da aka tura kan iyakokin ya shaida wa sashen Hausa na BBC a jiya Lahadi cewa: “Muna cikin wani mawuyacin hali. Tun gwamnatin Shugaba Buhari aka tura mu kan iyakokin kasa, amma duk da haka, ba mu samu alawus din mu ba tsawon shekara biyu da rabi.”
Ma’aikatan, wadanda suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana yanayin rayuwarsu a matsayin abin bakin ciki, tare da yin kira ga hukumomi da su magance halin da suke ciki.
Ya ci gaba da cewa, “Da farko an tura mu ne tare da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an DSS. Ana biyan mu dukkan alawus-alawus akan lokaci kafin daga bisani abubuwa su taɓarɓare.
“Ba a biya mu alawus ba na tsawon wata 30. Hakan ya fara ne a kwanaki na karshe na Shugaba Buhari.
Da ya ke mayar da martani a lokacin da ya ke zantawa da Daily Trust, Kakakin Hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada ya ce hukumar ta san halin da ake ciki kuma tana yin wasu gyare-gyare ne akan lamarin.
Shi kuma kakakin hukumar NIS, Kenneth Udo, bayan an tuntube shi, ya yi alkawarin yin bincike tare da tuntubar Daily Trust nan gaba.