
Victor Umeh, Sanata mai wakiltar Anambra to Tsakiya baiyana cewa a halin yanzu dai jam’iyyar Labour (LP) ba ta da shugabanci a Nijeriya.
Ya baiyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Siyasa a Yau a gidan talabijin na Channels.
Umeh, wanda kusa ne a LP, ya fadi hakan ne a yayin da aka yi masa tambaya akan rikicin da ke jam’iyyar ta labour.
Hakan na zuwa ne yayin da dan takarar shugabancin ƙasa a LP a zaɓen 2023, Peter Obi ke kokarin kawo sauyin a shugabancin jam’iyyar a fadin ƙasa.