
Kungiyar matasa ta Ohanaeze Ndigbo a fadin duniya ta wanke shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu akan ƙarin farashin man fetur na kwanan nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin shugaban kungiyar na kasa, Chukwuma Okpalaezeukwu ya fitar a Abuja a jiya Lahadi.
Okpalaezeukwu ya yaba da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke yi na sake fasalin harkar man fetur, inda ya kara da cewa karin farashin man fetur na daya daga cikin matakan sauya fannin domin amfanin kasa baki daya.
Okpalaezeukwu, wanda ya dora alhakin matsalar man fetur a kan rashin shugabanci na gari da rashin gudanar da ayyukan daga gwamnatocin da suka gabata, ya ce hakan na daga cikin kudurin da kungiyar ta yanke bayan taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 52 a Abuja.
A cewarsa, gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba ita ce ta haddasa matsalar man fetur ba.
Sai dai kuma kungiyar ta bayyana kwarin guiwar cewa karin farashin man fetur na kwanan nan zai sauya yadda ya kamata, biyo bayan manufofin tattalin arziki da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa.