
Gwamnatin jihar Borno ta yi kira ga al’umma da su gaggauta tashi daga wajen da ambaliyar ruwa ta mamaye a birnin Maiduguri
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Farfesa Usman Tar ya fitar a safiyar yau Talata.
Ya ce “Sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu a wannan shekara, muna kira ga mutanen da ke zaune kusa da koguna da su tashi nan take domin kare kansu da kuma dukiyoyinsu.
BBC Hausa ta rawaito cewa tituna da dama ne dai su ka cika maƙil da ruwa wanda hakan ya janyo wahala wajen zirga-zirgar ababen hawa.
Hakazalika ambaliyar ruwan ta tilasta wa dubban mutane barin muhallansu a Maidgurin.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da madatsar ruwa ta Alau ta ɓalle, bayan cikar da ta yi tsawon mako ɗaya.