Home Labarai Tinubu ya bada umarnin gaggauta kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri

Tinubu ya bada umarnin gaggauta kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri

0
Tinubu ya bada umarnin gaggauta kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna damuwa kan ambaliyar ruwa da ta shafi birnin Maiduguri na jihar Borno.

Ambaliyar ruwan wacce ba a samu irin ta tsawon shekaru ba a jihar ta raba dubban mutane da muhallansu, inda kuma ta shafi wurare da dama ciki har da asibitin koyarwa na Maiduguri.

A wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na mussaman kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yi jaje ga gwamnati da al’ummar jihar ta Borno.

“Yayin da hukumomi ke tantance barnar da ambaliyar ta haifar, shugaban kasa ya yi kira da a gaggauta dauke mutane daga wuraren da abin ya shafa.

” Shugaban kasa Tinubu ya tabbatarwa da Gwamna Babagana Zulum cewa Gwamnatin tarayya a shirye take wajen hada kai da jihar don samar da agajin gaggawa ga al’ummar da abin ya shafa”, inji sanarwar.

Haka kuma, shugaban kasar ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta kai kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwan ta sha fa.