Home Labarai Ambaliya: Al’umma sun fara komawa mahallansu yayin da ruwa ya fara janye wa a Maiduguri

Ambaliya: Al’umma sun fara komawa mahallansu yayin da ruwa ya fara janye wa a Maiduguri

0
Ambaliya: Al’umma sun fara komawa mahallansu yayin da ruwa ya fara janye wa a Maiduguri

Mazauna garin Maiduguri da ruwa ya raba da muhallansu daga madatsar ruwa ta Alau sun fara komawa gidajensu yayin da ruwan ke raguwa a hankali.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa da yawa daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa da suka kwana a waje sun ce duk da cewa ruwan ya lafa, suna son tantance asarar da suka yi ne a gidajen na su.

“Muna gaggawar ganin abin da ya rage na gidajenmu da kuma kwashe sauran abubuwan da su ka rage daga dukiyoyinmu da har yanzu za mu iya amfani da su,” in ji Ali Bana da ake unguwar Gwange.

Shi ma Musa Abdullahi na unguwar Gomari, ya ce ya samu damar zuwa gidansa.

“Har yanzu gidana ya na cike da ruwa. Duba da yanayin, gaskiya sai mun kara kwanaki a waje kafin mu koma gidajen mu” in ji Abdullahi.

Hukumomi sun ce fiye da mutane 239,000 ne ambaliyar ta shafa.

“Ambaliyar ta tilasta wa wasu mutanen da abin ya shafa kaura kai tsaye zuwa sansanin yan gudun hijira na Muna, wanda tuni akwai ‘yan gudun hijira sama da 50,000 a cikin sa.