
Dubun wani tsoho ɗan shekara 74 ta cika, inda aka kama shi yana satar tabarmin masallatai a Jihar Kaduna.
Aminiya ta rawaito cewa tsohon dai ya amsa cewa ya shafe sama da shekaru 10 yana shiga masallatai ya sace tabarminsu.
Ya kara da cewa wani lokaci ma yakan saci agogon bangon masallatai, amma bai taɓa satar Alkur’ani ba.
An kama wannan tsoho yana satar tabarmin ne a wani ƙaramin masallaci da ke unguwar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi.
Dubunsa ta cika ne a masallacin da ke layin Sarkin Bori Sule, a ranar Talata, bayan an addabi masallatan unguwar da satar sabbin tabarmi.
Mutumin ya kuma amsa cewa karo na biyu ke nan da ya saci tabarmi daga masallacin da aka kama shi.
Ya ce, “Da ni ake sallar jam’i, idan mutane suka fice sai in dauke sabbin tabarmi. Nakan sayar da kowacce a kan N1,500 zuwa N2,000.”