Home Labarai Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Kano — APC

Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Kano — APC

0
Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Kano — APC

Jam’iyyar APC a jihar Kano tace za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa.

A sanarwar da kakakin jam’iyyar, Hon. Ahmad S Aruwa ya fitar yace bayan karbar rahoton kwamitin da ya tattara shawararwari don shiga zaben, jam’iyyar ta yanke hukunci shiga a matsayinta Na jam’iyya mai mulki a Najeriya.

Sanarwar ta kuma umarci dukkanin masu sha’awar takarar su kai takardar nuna sha’awa ga ofishin jam’iyyar dake kananan hukumomi tun daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Satumba.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya jam’iyyar APC ta jihar kano ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Rabi’u Sulaiman Bichi, domin su duba yiwuwa jam’iyyar ta shiga zaben ko kar ta shiga.

Daga karshe dai a jiya laraba kwamiti ya mika rahotonsa, kuma ga shi a yau jam’iyyar ta amince zata shiga a fafata da ita a zaɓen shugabannin kananan hukumomin dake tafe.