Home Labarai Mutane 4 sun rasu kuma 36 na kwance a asibiti sakamakon ɓarkewae cutar kwalara a Yola

Mutane 4 sun rasu kuma 36 na kwance a asibiti sakamakon ɓarkewae cutar kwalara a Yola

0
Mutane 4 sun rasu kuma 36 na kwance a asibiti sakamakon ɓarkewae cutar kwalara a Yola

An samu barkewar cutar kwalara a karamar hukumar Yola-ta-Arewa a jihar Adamawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu tare da kwantar da mutane 36 a asibiti, a cewar Jibrin Ibrahim, shugaban ƙaramar hukumar.

Ibrahim ya bayyana hakan ne ga manema labarai yayin wata ziyara da ya kai wa wadanda lamarin ya shafa a cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa (IDC) da ke Yola, a yau Lahadi.

Ya bayyana cewa cutar ta barke ne a unguwannin Alkalawa, Ajiya, da Limawa da ke cikin ƙaramar hukumar.

Bayan isowarsa, Ibrahim ya ba da rahoton cewa an fara samun mutane 20 da suka kamu da cutar, amma adadin ya karu da sauri zuwa 40, yayin da hudu su ka rasu.

Ya yi nuni da cewa an kwantar da marasa lafiya da dama kuma suna samun kulawar likitoci daga ma’aikatan lafiya.

Shugaban ya kuma yaba da saurin martanin da ma’aikatan lafiya, Red Cross, da abokan hulda na kasa da kasa suka bayar wajen magance barkewar cutar.