Home Labarai Gwamnatin Kano ta bada tallafin Naira Miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Gwamnatin Kano ta bada tallafin Naira Miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

0
Gwamnatin Kano ta bada tallafin Naira Miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Gwamnatin jihar Kano ta bada tallafin Naira Miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye ne ya mika cak na kudin tare da kwamishiniyar jinkai, Amina Sani a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gwamna Babagana Zulum ne ya karbi wakilan gwamnan a gidan gwamnatin jihar Borno.

Abba Yusuf, ya jajantawa wadanda abin ya shafa inda ya bayyana amabliyar a matsayin babban bala’i.

Yayi kira da a kara tallafawa mutanen da kuma bayani kan alfanun hada karfi da karfe wajen magance irin wannan ambaliyar.

Abba Kabir Yusuf ya kuma jaddada goyan bayan jihar Kano ga al’ummar Borno a wannan yanayi da suke ciki.

Gwamnan ya kuma yi addu’a ga wadanda suka rasa ransu da addu’ar neman sauki ga wadanda suka jikkata.

Anasa jawabin, Gwamna Zulum ya godewa Gwamnatin jihar Kano bisa tallafin da ta basu.