Home Labarai Ƴan bindiga sun kashe mutanen da su ka sace tare da waɗanda su ka je kai kuɗin fansa a Neja

Ƴan bindiga sun kashe mutanen da su ka sace tare da waɗanda su ka je kai kuɗin fansa a Neja

0
Ƴan bindiga sun kashe mutanen da su ka sace tare da waɗanda su ka je kai kuɗin fansa a Neja

Waɗanda su ka yi garkuwa da wani mamallakin otel da manajan sa da wasu baƙi a garin Gauraka da ke ƙaramar hukumar Tafa a jihar Neja sun kashe su bayan karɓar kuɗin fansa na Naira Miliyan 25.

Daily Trust ta ce rahotanni sun bayyana cewa ƴan fashin dajin sun kuma kashe mutane biyu da su ka kai kuɗin fansar.

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Tafa, wanda ɗan uwa ne ga daya daga cikin waɗanda aka kashe, Yau Ahmad, ya ce an kashe mutanen ne a dajin Dogon -Daji wanda ke iyakar Kaduna da Neja da birnin tarayya Abuja.

Ya ce an kai gawarwakin mutanen zuwa ofishin rundunar sojan-sama da ke kusa da filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja bayan gano gawarwakin a dajin.

Kwamandan ƴan bijilanti a karamar hukumar Tafa, Hussaini Abubakar ya ce an binne gawar mutane biyu da suka kai kuɗin fansa waɗanda mambobin su ne bayan amincewar sojoji.

Jaridar Daily Trust ta rawaito yadda aka sace mutanen a ranar 17 ga watan Agusta.

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun kai farmaki da karfe 1 na dare otel din inda su ka sace duk baƙin da su ka kama ɗaki.