
Yayin da zaben gwamnan jihar Edo ke kara karatowa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce zaben jam’iyyar APC a jihar zai zama cewa ƴan jihar sun ɗebo ruwan dafa kan su.
Ya bukaci masu kada kuri’a da su tambayi kansu shin APC ta kyautata rayuwa ne, ko kuma ta kara zafafa rayuwar su kafin kada kuri’a.
Punch ta rawaito cewa Atiku ya kuma ce jam’iyyar APC ta jefa Najeriya cikin wani mawuyacin hali na wahala tare da shuka tsaba ta fatara da yunwa da rashin tsaro.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba mai taken ‘Zabi na gari don cigaban Edo a baiyane ya ke.”.
“Sun soki gwamnatocin baya kan kara farashin man fetur, amma a yau, sun jagoranci zamanin da farashin man fetur ya haura N900 kan kowace lita. Zalunci da rashin kula da halin da talakawa ke ciki ba ya misaltuwa.
“Kuri’ar APC kuri’a ce ta ci gaba da kunci, yunwa, da fidda rai,” Atiku, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya ce.