
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Ƙasa, NECO za ta saki sakamakon jarrabawar 2024 a gobe Alhamis.
Wata majiya mai tushe a hukumar ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA cewa, hukumar ta kammala shirin sakin sakamakon jarrabawar a gobe.
Acewar majiyar, Rijistaran hukumar ne ake
sa ran zai sanar da sakamakon da misalin karfe 12 na rana.
Dalibai dai sun zana jarrabawar ne a watan Yuni da Yuli na shekarar da muke ciki.