Home Labarai Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban kasa

Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban kasa

0
Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban kasa

Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na wannan shekara ba.

Don haka, a wata sanarwa da Bayo Onanuga,
mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman, Tinubu ya umarci mataimakin sa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya.

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu, wanda ya koma kasar a ranar Lahadin da ta gabata bayan tafiyarsa zuwa kasashen China da Birtaniya, yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida da kuma magance wasu kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman bayan da aka yi fama da bala’in ambaliyar ruwa.

A taron Majalisar Dinkin Duniya 79, mataimakin shugaban kasa Shettima zai gabatar da bayanin kasa Najeriya ga babban taron, da halartar muhimman abubuwan da suka faru a gefe, da kuma gudanar da tarukan kasashen biyu.

Babban Muhawara mai taken “Kada a bar kowa a baya: Yin aiki tare don ci gaban zaman lafiya, dauwamammen ci gaba da mutunta bil’adama na yanzu da na gaba” zai gudana ne daga ranar Talata 24 ga watan Satumba zuwa ranar Asabar 28 ga watan Satumba. 2024.

(